Hausa Novels

Maganin Ciwon Kai Mai Sauki

Maganin Ciwon Kai Mai Sauki

Ciwon kai yana daga cikin cututtuka da ake fama da su a rayuwarmu ta yau-da-kullun wadanda suka addabi jama’a. Mafiya yawan mutane sukan yi ciwon kai akalla sau biyu ko uku, ko fiye da haka a cikin kowanne wata.

Migraine

Kanumfari: Wanda ya ke fama da ciwon kai irin na Mura ko sanyi, ko Jiri, ya nemi garin Kanumfari cokali biyu ko Uku, ya dafa shi da ruwa. Bayan ya dafu sai a sanya ruwan Khal cokali biyu, a sanya Sukari sannan a sha.

In sha Allahu koda majina ce ta daskare a cikin kirjin mutum to za a samu sauki da izinin Allah.

Kabewa: Kabewa idan aka dafa, ka samo ruwanta ka hada da Sukari ka rika sha. In sha Allahu yana magance yawan ciwon kai.

Kuma Namiji wanda yake fama da rauni wajen biyan bukatar iyalinsa, ko kuma Mace wacce take fama da matsalar daukewar sha’awa, ko Bushewa za su samu sauki.

Haka nan mutumin da zuciyarsa take yawan bugawa da karfi shi ma idan yana shan ruwan kabewar zai samu sauki in sha Allah.

Habbatus Sauda: Ka samu rabin kofi na ‘ya’yan Habbatus sauda, Kanumfari cokali biyu, Yansun ma rabin kofi. A hada su a daka a turmi. Sannan a rika diban cokali biyu ana dafawa da ruwa kofi daya. Idan ya dahu sai a bar shi ya huce, sannan a zuba zuma, a rika sha.

Masu ciwon kai, Masu Olsa (Ulcer), Masu hawan Jini, Masu ciwon kirji, Masu tsakuwar koda, idan suna shan wannan za su samu lafiya da izinin Allah. Za a rika sha safe da yamma ne.

Lemon Zaki: A samu bawon Lemu a yanyanka shi kamar cikin kofi guda, a dafa shi da ruwa kofi biyu. Idan ya tafasa sai a sauke. A tace da rariya sannan a sanya zuma a rika shansa safe da yamma.

Masu Ciwon kai da masu fama da kumburin ciki ko rashin narkewar abinci za su samu lafiya.

Na’a-Na’a : A samu ganyen Na’a-Na’a, Ganyen Raihan, a dafa su tare da kanumfari a rika sanya zuma, ana shan ruwan da duminsa, sannan a rika goga ganyen a kan goshin marar lafiyan.

Wannan maganin Ciwon kai ne sadidan, kuma yana magance cutar kumburin jiki, yana magance ciwon sanyi na mata, yana magance ciwon daji (Cancer). In sha Allahu.

Sana-Makkiy : Cokali uku na sanamiki, Cokali uku na garin Habbatus Sauda, Cokali biyu na chitta a hada su a dafa da ruwa kofi biyu sannan a sanya sukari a rika sha safe da yamma. Sannan a rika shafa Man Chitta (Ginger Oil) a kan goshin marar lafiyan.

In sha Allahu kai zai daina ciwo. Idan kuma Jiri ne ko Hajijiya shi ma za a samu lafiya in sha Allah.

Man Habbatus Sauda: A rika shafawa akan marar lafiyan in sha Allahu kan zai daina ciwo. Amma za a rika maimaitawa safe da rana da yamma.

Man Raihan: A hada man raihan da Man Hasa-lebban, tare da turaren Wardi a hada waje guda a rika shafe jikin marar lafiyan baki daya. Bayan an karanta Fatiha 7, Ayatul kursiyyi 7, Suratul Feel 11, Kul Huwallahu 11, Falaki da Naasi 11 a tofa a cikin wannan hadin.

In sha Allahu wannan maganin ciwon kai ne sosai, musamman irin wanda Shaidanun Aljanu suke haddasawa. Kuma yana magance ciwon jiki ko shanyewar gabobi irin wanda Aljanu ke sanyawa.

Furen Albabunaj : Idan aka tafasa cokali biyu, ana shansa safe da yamma kamar shayi, in sha Allahu za a ga abun mamaki wajen samun waraka daga ciwon kai, ciwon koda, rashin barci, faduwar gaba, makalewar fitsari, da sauransu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button