Hausa Novels

Muhimmanci shan zobo a lokacin Azumin Ramadan.

Muhimmanci shan zobo a lokacin Azumin Ramadan.

Zobo na daya daga cikin abubuwan sha da ake anfani da su a cikin watan azumin Ramadan, wanda yake kunshi da muhimman sinadirai masu yawa wadanda ke ba shi fa’idodi iri-iri.

Daga cikin fa’idodin amfani da zobo ga mai azumi sun hada da.

● Saukar da hawan jini: Zobo yana taimakawa wajen magance cutar hawan jini, sannan kuma baya ga haka, yana aiki a matsayin diuretic.

● Rage matakin cholesterol na jini: musamman ga mutanen dake fama da ciwon sukari wato diebetes.

● Rage sukarin jini: Zobo ana daukar sa daya daga cikin abin sha da ake amfani dashi a Ramadan mai matukar tasiri ga masu ciwon sukari, amma yana da kyau a kula da amfani dashi idan kuna shan magungunan rage sukarin jini.

● Maganin Cushewar ciki: Bugu da kari, yana da tasiri sosai akan wasu matsalolin tsarin narkewar abinci kamar su rashin cin abinci da ciwon ciki, sannan kuma yana taimakawa wajen inganta narkewar abinci.

● Rage kiba: Zobo yana iya iya taimakawa wajen rage kiba ta hanyar rage adadin yawan sukari da jiki ke diba daga ciki.

● Kula da lafiyar hanta: Zobo yana aiki don bada rigakafi da magance wasu cututtukan hanta saboda yana ɗauke da antioxidants properties.

● Rage ciwon haila: yana kuma taimakawa wajen sassaita hormonal balance a cikin jiki da kuma alamomin da ke da alaqa da haila.

● Rage kishirwa: Lokacin da mutum yasha zobo mai sanyi, yana taimakawa wajen rage ƙishirwa da kuma sanyaya jiki da hana shi bushewa.

Don shirya zobo, ana zuba shi rabin kofi a cikin kwanon da aka cika shi da tafasasshen ruwa, a jika shi na tsawon rabin sa’a, sannan a tace shi, sai a sha da zafin sa ko kuma a sanyaya shi, anso ayi amfani da zuma kadan wajen kara masa zaki.

Duk da fa’idodin da zobo yake dasu, ya kamata a yi taka tsantsan yayin amfani da shi a cikin waɗannan lokuta:

■ Lokacin ciki da shayarwa

■ Lokacin da ake shan magungunan masu saukar da sukarin jini

■ Lokacin hormonal treatment

■ Da wadanda idan sun sha zobon yake haifar musu da matsala.

ALLAH YA KARBI IBADUN MU.

INA NEMAN ALFARMAR KU SANI ACIKIN ADDU’OI KU A LOKACIN WANNAN IBADA MAI GIRMA DA DUKA SAURAN BAYIN ALLAH, ALLAH YA BIYAWA KOWA BUKATUN SA NA ALKHAIRI.

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button