Amfanin Sabaya a jikin mace

AMFANIN SABAYA GA JIKIN MACE
Sabaya na daya daga cikin kayan abinci da ke da matukar amfani ga lafiyar mace, musamman bayan haihuwa. Yana taimakawa wajen dawo da halittar jiki kamar yadda Allah Ya halicce ta.
Amfanin Sabaya
1. Kare Nonon Mace Daga Zubewa
Yawan amfani da sabaya yana taimakawa wajen tabbatar da cewa nonon mace ba zai zube ba, yana taimakawa wajen tsaftace tsarin jikinta.
2. Yana Sanya Jiki Laushi
Idan mace tana amfani da sabaya, jikinta zai kasance mai laushi da kyau kamar jarirai.
3. Kare Mace Daga Yin Rama Bayan Haihuwa
Mafi yawan mata na ramewa bayan haihuwa, amma sabaya na taimakawa wajen hana mace ramewa da saurin dawowa da kuzarin jikinta.
4. Yana Kara Yawan Ruwan Nono
Ga mata masu shayarwa, sabaya na kara yawan ruwan nono, yana taimakawa wajen gina lafiyar jariri.
5. Kariya Ga Jariri
Yaron da ya sha nonon uwa da ke amfani da sabaya yana samun kariya daga cututtuka.
6. Yana Kara Lafiyar Magidanci
Idan magidanci ya sha, yana kara masa lafiya da kuzari, har ma wajen kusantar iyalinsa.
—
Abubuwan da Ake Bukata Wajen Hada Sabaya
Alkama – Mudu 1
Danyen Shinkafa – Mudu 1
Waken Suya – Mudu 1
Ridi – Mudu ½
Hulba – Mudu ½
Gyada mai bargo/Kamfala – Yawan da ya dace
Madara – Gwargwadon bukata
Zuma – Gwargwadon bukata
—
Yadda Ake Hada Sabaya
1. A hada ridi da gyada, a soya ridin yadda ake kantu, sannan a soya gyadar yadda ake yin ƙuli-ƙuli.
2. Shinkafa da alkama a jika su na tsawon awa 5, sannan a shanya su.
3. A hada dukkanin abubuwan (ridi, gyada, alkama, hulba, da shinkafa) wuri guda.
4. A kai su a niƙa a zama gari mai laushi sosai.
5. Mata masu ciki na iya fara amfani da shi tun kafin su haihu har bayan haihuwa domin samun fa’idarsa sosai.
—
Yadda Ake Sha
A dama shi kamar yadda ake hada kunu.
Bayan an zuba ruwan zafi, ana iya maidawa kan wuta na dan lokaci.
Ana iya shan cokali uku a rana, tare da hadawa da zuma da madara.
Idan magidanci zai sha, sai a kara yawan cokali zuwa shida.
—
Sabaya na da matukar amfani ga lafiyar mace da kuma magidanci. Yana taimakawa wajen inganta lafiyar jiki, hana ramewa bayan haihuwa, da kuma bunkasa kuzari. Allah Ya sa a amfana!