Hausa Novels

SAKO ZUWA GA MATAN AURE ZALLAH

╭───── • ༄༂ • ─────╮⁣⁣
💌SAKON ZUWA GA MATA💌
╰───── • ༄༂ • ─────╯⁣

Idan Ke Mace ne, Toh Ki Karanta Wannan Saqon Akan Aure.

1. Shi aure ibada ne, duk abinda aka ƙira shi da ibada dole akwai wahala cikin yin sa, dole sai an daure sai an cije an kuma yi hakuri.

2. Aure yana tattare da jarrabawa, wanda mutuwa ce kawai ke iya ganin karshen wannan jarabawar, dole a jarabce ku cikin lamuran ku, kamar yadda Allah yace.

3. Kiyi hakuri da mijin da Allah ya haɗaki da shi, matukar zai iya ciyar dake, shayar dake da kuma sauke hakkin kwanciyar aure dan wanna sune ginshikin bayan aure.

4. Indai mutum biyu zasu yi rayuwa, toh ya zama dole ɗaya ya kwari ɗaya, dole wani ya ɓoye wayon sa dan a zauna lafiya ba dan anfi shi wayon ba.

5. Babu wani abinda zai tabbata, musamman zaluncin ɗaya daga cikin ma’aurata dole wataran Allah yayi al’amarin sa, indai anyi hakuri toh za a ga karshen komai.

6. Ki sauƙe hakkin da yake akan ki, matsayin na mace Koh matar aure, kar ki yadda dan ba a sauke miki naki ba kema, ki ƙi sauke wa, kowa ƙabarin sa daban.

7. Aure cike yake da matsalolin da Allah kadai yasan iyakar su, ana daura miki aure yau, ki sanya a ranki kina iya shiga matsala ta har abada a kan sa.

8. Ba matar da ba ta fama da wata matsala a gidan miji, cikin 100, 5 ne kawai za a same su da sauki amma sauran ko wacce da nata kalar, kar ki dauka ke kadai ce  kike fama.

8. Allah ya rantse sai ya jarabce mu, kuma kowa da kalar ta sa jarabawar, dan haka ki dauki matsalar gidan miji a matsayin kaddarar ki.

9. Babu abinda ke zaunar da aure lafiya, kamar hakuri da kuma juriya, muddun kika lazunci wannan toh Insha-Allah wataran sai labari.

10. Idan har Allah ya albarka ce ku da samun Haihuwa, nan ne zaki nin ka juriyar ki, watarana yaran nan da kika haifah zasu ƙwatar miki da ƴan cin ki.

11. Ki riƙe sana’ar ki sa kyau, Idan kina yi, idan bakya yi, ki samu wanda yayi dai-dai da inda kike ki yi. Kar ki zauna ba sana’a.

12. Kar ki yi wasa da tarbiyyar yaran da kika haifa Koh da kuwa mahaifinsu bai damu ba, yaran ki sune kadarar ki na ƙarshe.

13. Wajen zaɓan miji, ki rufe idanun ki, kar ki ɓiyewa zuciyar ki. Kiyi amfani da kwakwalwar ki, domin Rayuwar ki ce zaki miƙata ma wani kuma na har abada.

14. Namiji na iya komai, wajen ganin ya burge wacce yake so kafin ya aure ta domin kar wani ya burgeta ya kuma samu kusan ci da ita fiye da shi.

15. Bayan aure, mace zata koma matsayin namiji, shi kuma ya koma matsayin ta. Ita ce, zama zakiyi ki burge mijin ki da duk abinda kika alamun yana so dan mallake shi gaba-daya.

16. Sa’ar miji yafi Sa’ar komai,  Ki bar duk abinda kike yi, matukar kin samu mijin da ya dace, kiyi auren ki, mijin ki zai kare dukkan muradun ki, kuma kece farko cikin lissafin sa.

17. Miji nagari, ba zai ɓukaci komai daga gare ki ba, kama daga jikin ki, dukiyar ki, ba kuma zai yi nisa daga in da kike ba, duk yadda rayuwa zata sauya.

18. Kar ki yadda, kiyi aure da alhakin wani namiji akan ki, wani bakin shi yafi guba lalata komai, ki tabbatar kin wanye da kowa kalau.

19. Zaɓin iyaye shine zaɓin da yafi kowani zaɓi nagarta a aure, koyi hakuri ki kuma yi addu’a, Koh kuwa kina da wanda kike so, ki bi nasun dan sun fi ki hangen nesa.

20. Ki kyautata wa kowa dake da alaka da mijin ki, musamman iyayen sa hakan zai sa, su dawo tsaginki Koh da kuwa ya nemi ya tozarta ki zasu tsaya miki.

Idan kin karanta saqon nan, kiyi sharing ɗin sa zuwa ga ƴan uwan ki mata, wata ƙila su amfana bayan sun karanta.

Inda mata zasu yi hakuri da zaluncin da mazajen su ke musu a gidajensu na aure, zasu riga mazajen su sa yawa shiga aljanna, amma ina 😓

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button